Ephesians 1

1Wasiƙa daga Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yǎ zama manzon Kiristi Yesu.

Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa,
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā ba su da a Afisa.
da suke amintattu
Ko kuwa masu bi waɗanda
cikin Kiristi Yesu:

2Bari alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.

Albarkun Ruhaniya a cikin Kiristi

3Yabo ya tabbata ga Allah da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4Tun dā can, kafin ma a halicci duniya Allah ya zaɓe mu a cikin Kiristi don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5A cikin ƙauna, ya
Ko kuwa gani cikin ƙauna. 5 Ya
ƙaddara mu mu zama ʼyaʼyansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu. Wannan kuwa ya sa ya ji daɗi.
6Don haka muna yabon Allah saboda alherin da ya yi mana domin mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. 7Ta wurin mutuwar Kiristi ne muka sami ʼyanci, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8wanda ya ba mu ba iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yǎ cika ta wurin Kiristi. 10Saʼan nan da lokaci ya yi, Allah zai yi duk abin da ya shirya, kuma Kiristi zai kawo kome da yake a sama da ƙasa a ƙarƙashin ikonsa.

11Saboda Kiristi ne muka sami gādo daga Allah,
Ko kuwa mun zama abin gādon Allah.
gama ya zaɓe mu daga farko, kome kuma ya faru yadda ya shirya tuntuni.
12Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi ne, za mu yabi ɗaukakar Allah. 13Kiristi ya kawo muku gaskiya, wadda take labari mai daɗi game da yadda za ku sami ceto. Kun sa bangaskiyarku a cikin Kiristi aka kuwa yi muku alkawarin Ruhu Mai Tsarki don a nuna ku na Allah ne. 14Ruhu Mai Tsarki shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari kuma cewa mu mallakarsa ce. Wannan shi ne wani dalilin da za mu yabi Allahnmu mai ɗaukaka.

Godiya da Adduʼa

15Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka, 16ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin adduʼoʼina. 17Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai ɗaukaka, yǎ ba ku Ruhunsa. Ruhun kuwa zai ba ku hikima yǎ kuma sa ku gane abin da ake nufi da sanin Allah. 18Ina kuma adduʼa cewa zuciyarku ta waye don ku gane begen da aka ba ku saʼad da Allah ya zaɓe ku. Saʼan nan ne za ku gane albarku masu ɗaukakan da za su zama naku tare da dukan tsarkaka. 19Ina so ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali wanda yake namu. Da wannan ikon nan mai girma ne 20ya ta da Kiristi daga matattu ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta da iko da ƙarfi da mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. 22Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi wannan iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. 23Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

Copyright information for HauSRK